A jiya ranar larba shugaban kasar Nijar ya karrama hadiman shugaban kasa Muhammadu Buhar guda biyu, Lawal Kazaure da kuma Sarki Abba.
Yayin da kuma ya karrama Aliko Dangote da Abdulsamad mai kamfanin BUA tare da gwamna Abubakar Badaru na Jigawa da kuma Matawallen Zamfara.
Shugaban Nijar, Mohammed Bazoum ya basu kyautar karramawa da kuma jinjina a taron bikin zagayowar ranar samun ‘yanci ta kasashen yammacin Afrika karo 62.
Kuma yace Najeriya ita ce kasa mai kusanci dasu sannan kuma itace babbar kawar Nijar a Afrika, domin tana taimaka mata wurin warware matsalolinta na cikin gida.