fbpx
Tuesday, July 5
Shadow

Jami’an Custom sun kwace wasu kayayyaki na kimani naira miliyan 265 a jihar Katsina

Hukumar custom ta Najeriya reshen jihar Katsina, ta ce ta kwace wasu kayayyakin sama da naira miliyan 265 daga watan Afrilu zuwa yau.
Kwamandan rundunar Yankin, Kirawa Abdulahi, wanda ya bayyana hakan ga manema labarai jiya a hedikwatar rundunar da ke Katsina, ya ce kamon kayak ya samo asali ne daga tattara bayanan sirri da kuma aiki tare da sauran ofishushin na hukumar.
Ya ce, “A cikin watan Afrilun 2020 zuwa yau an yi jigilar kayayyaki 166 tare da ababen hawa 65 (wanda ake anfani da su gurin jigilar kayayyakin) darajan DPV na naira miliyan 265, 746,400.00” Wasu daga cikin abubuwan da aka kama sune: jaka 2,327 na shinkafar kasashen waje 50k, 1,106 Jarkokin man girki masu girman lita 25, katon 2,711 na taliya, motocin 4 da aka yi amfani dasu (Tokunbo), buhun kanwa 600, abubuwan hada kayan sawa 228 na kowane irin, abubuwan hada kayan sawa wanda anyi anfani da su 154, katunan 19 na turare. ”
Don haka ya tabbatar da cewa duk abin da ke kan iyaka an haramta shi, saboda gwamnati ta rigaya ta rufe iyakar amma masu shugoda kayan ta barauniyar hanya a koyaushe suna nemo hanyoyin shigo da kayayyaki, dauke da su a babura, motoci ko shiga da kafafu. Abdulahi ya gargadi masu fasakwarin da su daina kamar yadda rundunar a shirye suke su bi damke su.

Dan sauke manhajar hutudole a wayoyin ku. Sai a bi wannan link din na kasa:

Karanta wannan  Mutane 18 sun mutu sakamakon hadarin mota akan babbar hanyar Legas zuwa Ibadan

Leave a Reply

Your email address will not be published.