fbpx
Monday, March 1
Shadow

Jami’an Kwastam 3 ne Boko Haram suka sace a harin da suka kai Geidam jihar Yobe

Rahotanni daga harin da Boko Haram suka kai jihar Yobe na kara fitowa inda a yanzu aka samu cewa sun dade a garin Geidam, sai tsakiyar dare sannan suka fita.

 

BBChausa ta zanta da wasu mazauna garin inda suka ce Boko Haram ta fasa shaguna ta kwashi kaya sannan kuma ta tafi da wasu jami’an kwastam 3.

 

Da yake magana akan Lamarin, kakakin ‘Yansandan jihar Yobe, ASP Dungus Abdulkarim ya bayyana cewa Sojojin Najeriya sun kai dauki daga baya inda suka yi artabu da Boko Haram din suka fatattake su.

 

Yace kuma akwai Rahoton dake cewa sun tafi da jami’an kwastam 3 amma basu kai ga tabbatar dashi ba tukuna.

 

Rahoton yace Boko Haram ta kafa sabbin sansanoni a kauyukan Yusufari inda daga nan ne take shiga tana kai hare-hare.

Dan sauke manhajar hutudole a wayoyin ku. Sai a bi wannan link din na kasa:


×
Kano

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *