Friday, May 29
Shadow

Jami’an tsaro sun ci Amanar mu>>El-Rufai

 

Bayanin Gwamnan Jihar Kaduna a yau da yayi kai tsaye inda yawa jama’ar jihar jawabi kan dokar cutar Coronavirus/COVID-19 yayi bayanai da yawa, saidai gwamna ya nanata bada hakuri ga jama’ar jihar Kaduna da kuma godiya ga yanda suke bin dokar.

 

Ga wasu daga cikin bayanan da gwamnan yayi a jawabin na yai kamar haka:

 

Gwamnan yace sun dauki Teleli 1500 dan dinka abin rufe hanci saboda akwai wanda basa iya sayeshi saboda babu, yace za’a yi abin rufe hanci da baki Miliyan 2 dan rabawa Talakawa da masu kananan sana’o’i.

 

Matakan da muka dauka a jiharnan shiyasa bamu da wannan mace-macen.

Gwamnan ya kuma yi bayanin cewa idan jama’ar jihar Kaduna zasu saurari abinda ke faruwa a jihohi ma kwabta zasu ga cewa ba’a samun mace-macen da ake samu a wadancan jihohi a Kaduna. Yace matakan da suka daukane suka sa haka.

 

Ba dan Almajiran da aka kawo mana daga Kano ba da bamu samu yawan masu cutar Coronavirus/COVID-19 din da muke dasu ba.

 

Gwamna El-Rufa’i yace su kansu basa son wannan zaman gida da ake saboda kudin shiga basa zuwar musu, suna samun kudin shiga Miliyan 100 da wani abu. Yace amma mutane na zaune a gida basa aiki ana biyansu albashi suma ba son ransu bane.

 

Ya damu Gwamnati ya damu kowa.

 

Wane matakai ya kamata mu dauka kamin mu bude.

 

Gwamnan yace akwai sauran kayan aiki da basu zo jihar ba yace Na’urorin da muke dasu basu isar mu aiki. Yace dan haka

 

Muna godiya ga al’ummar jihar Kaduna da hakurin da suke ci gaba da yi.

 

Leburori masu gine-gine suna ci gaba da aiki.

 

Muna duba yanda za’a sassauta.

 

Duk ciwukan da muka samu daga wajan Kaduna aka zo dasu.

 

Jami’an Tsaro ake biya ana shigo da mutum

 

Jami’an tsaro sun ci amanarmu.

 

Ran sallah zan je hanyar Kano inga wanda zai shigo ranar

 

Wallahi wahalar da kukesha muma muna sha.

 

Sallah a yi a gida, Zumunci a yi a gida.

Dan sauke manhajar hutudole a wayoyin ku. Sai a bi wannan link din na kasa:

https://play.google.com/store/apps/details?id=hdlabarai.aplibwxLeave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *