fbpx
Tuesday, July 5
Shadow

Jami’an ‘Yan Sanda biyu sun rasa ransu Hadarin mota a Kwara

Jami’an ‘yan sanda biyu sun rasa rayukansu a wani hatsarin mota da ya rutsa da su bayan da motar da ke tafe da su ta afkawa wata tirelar da ke kan babbar hanyar Ilorin-Ogbomoso.
Jami’an suna dawowa Ilorin ne daga Ogbomoso inda suka yi wa motar banki.
“Jami’an ‘yan sanda suna dawowa daga Ogbomoso inda suka yi wata motat, ” in ji jami’in hulda da jama’a na’ yan sanda na Kwara SP Ajayi Okasanmi.
“Daya daga cikin tayoyin motar da ke rakiyar ta fashe sai ta afka cikin tirelar da aka ajiye a kan hanya.”
Dukkan jami’an biyu sun mutu nan take, amma wasu da hatsarin ya rutsa da su sun samu raunuka.
An ajiye gawarwakinsu a Asibitin Koyarwa na Jami’ar Ilorin, yayin da wadanda suka jikkata aka ce suna karbar kulawar likita a asibitin.
Shima kwamandan hukumar kiyaye haddura ta kasa (FRSC), Jonathan Owoade, ya tabbatar da faruwar lamarin.

Dan sauke manhajar hutudole a wayoyin ku. Sai a bi wannan link din na kasa:

Karanta wannan  Kungiyar magoya bayan Tinubu ta bayar da shawarar ya dauki Gwamna Elrufai a matsayin mataimakinsa

Leave a Reply

Your email address will not be published.