Jami’an ‘yansanda sun bayyana cewa suna neman Adamu Aliero Yankuzo dan kimanin shekaru 45 wanda shine shugaban ‘yan ta’addar dake aika-aika a tsakanin Zamfara da Katsina.
Kaamishinan ‘yansandan jihar Katsina, Sanusi Buba ne ya bayyana haka a ganawar da yayi da manema labarai.
Yace duk wanda ya kawo musu Adamu wanda dan Asalun Tsafene a rai ko a mace akwai ladar Miliyan 5.