fbpx
Sunday, February 28
Shadow

Jami’ar jihar Kaduna (KASU) ta ba da sharadin sake budewa a 25 ga watan Janairu

Jami’ar jihar Kaduna (KASU) ta ce a shirye take ta sake budewa a ranar 25 ga watan Janairun shekarar 2019/2020 karo na biyu na karatun ilimi idan aka ba ta amincewa.

Shugaban Jami’ar, Farfesa Muhammad Tanko ne ya bayyana hakan a Kaduna ranar Litinin yayin taron masu ruwa da tsaki kan sake bude makarantu, wanda Ma’aikatar Ilimi ta Jihar Kaduna ta shirya.
Tanko, wanda ya samu wakilcin Farfesa Yohanna Tella, Mataimakin Shugaban (Gudanarwa), ya bayyana cewa jami’ar za ta gabatar da lacca na tsawon makonni shida idan aka bari ta bude a ranar 25 ga Janairu.
Mataimakin shugaban jami’ar ya ce za a gabatar da laccoci ta ranar gizo ga manyan ajujuwa sama da dalibai hamsin ga daliban da ke matakin kasa da kuma laccocin zahiri ga kananan aji na dalibai hamsin na wadanda ke manyan ajujuwa.
Tanko ya ce, “Mun kuma tsara darussa masu na zahiri ga rukunna na kasa da dalibai 25 don kananan ajujuwa da 45 na manyan azuzuwan.
“Jarrabawar da za a yi wa daliban matakin 100 da na masu matakin karatu 200 za su kasance ne ta hanyar kwamfuta.
“Har ila yau, za mu horar da kuma wayar da kan ma’aikatanmu da dalibanmu game da kariya ta cutar COVID-19 da kuma bukatar nisantar da jama’a.”

Dan sauke manhajar hutudole a wayoyin ku. Sai a bi wannan link din na kasa:


×
Kano

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *