fbpx
Thursday, July 7
Shadow

Jami’in Hisban Da Aka Gani A Otel Da Matar Aure Ba Mai Laifi Ba Ne, Taimako Ya je Ya Yi, Cewar Rundunar ‘Yan Sanda Reshen Jihar Kano

Rundunar ‘yan sanda reshen jihar Kano ta wanke Jami’in hisban da a ke zargin ganin sa tare da matar aure a wani Otel.

 

Rundudunar ta bayyana haka ne ta bakin Kakakinta DSP Abdullahi Kiyawa wanda ya bayyana cewa”
Mun gamsu cewa ita wannan Yarinya kuntatawa da mijinta ke mata ne tayi sanadin fitowarta tana kokarin shiga Bariki. Shi Jami’in hisban da ake zargi ya je ya taho da ita ne ya yi kokarin ajiye ta a gidan wani, wanda Maigidan da aka ajiye ta daga baya ya dauke ta ya ce ai akwai inda ya kamata a ajiye ta tunda Otal din V.I.P ne ba kowa, shi kuma Jami’in hisban sai aka fada masa an kai ta Otal kaza shi kuma da ya ji haka shi ne ya sayi abinci ya je Otal din don ya ba ta. Mu kuma muna sintiri sai muka ji wani motsi wanda ba mu aminta da shi ba sai muka tattaro su, daga baya ne bayan mun gudanar da bincike muka gane ashe kusan ‘ya ce ma a wajensa, mijinta ne ya jefa ta cikin wani hali wanda ke kokarin haifar mata shiga karuwanci, shi ya taimaka ne don ganin cewa an kiyaye ta daga shiga Bariki.” Inji Haruna Abdullahi Kyawa.

Karanta wannan  "Dalilin dayasa ake cigaba da fuskantar matsalar tsaro a Najeriya":>>Atiku Abubakar

 

Batun ya janyo cece-kuce musamman ga wadanda ke nuna kiyayya ga aikin da hukumar hisban ke yi na yaki da mummuna da umarni da kyakkyawa, wanda suka yi ta kiran gwamnatin Kano da ta dauki mataki a kan Jami’in wanda hukumar ‘yan sanda ta ce ba mai laifi ba ne.

Dan sauke manhajar hutudole a wayoyin ku. Sai a bi wannan link din na kasa:

Leave a Reply

Your email address will not be published.