Hukukar jiragen kasa ta Najeriya, NRC ta bayyana cewa jami’n tsaro na tattaunawa da ‘yan Bindigar da suka sace mutane a cikin jirgin kasar dake jigila tsakanin Kaduna zuwa Abuja dan kubutar dasu.
Babban jami’in hukumar, Fidet Okhiria ne ya bayyana haka a ganawar da yayi da manema labarai inda yace kuma an kwaso wasu daga cikin sassan jirgin da suka lalace.
Yace jami’an tsaro suna kan tattaunawa da ‘yan Bindigar dan sako wadanda aka kama din. Yace iyalan wadanda aka kama suna tuntubarsu amma komai suna aikawa jami’an tsaron ne saboda ba aikinsu bane tuntubar ‘yan ta’addan.
Ya kuma godewa hukumomin tsaro kan hadin kan da suke basu wajan ganin al’amura sun daidaita.