Jam’iyyar APC ta bayyana gwamnan jihar filato, Simon La Long a matsayim darekta jamar na kungiyar kamfe ta Tinubu da Kashim Shettima.
Shugaban jam’iyyar APC Abdullahi Adamu ya bayyana hakan a fadar shugaban kasa Muhammdu Buhari dake babban birnin tarayya.
Inda yace sun zo neman izinin shugaba Buhari ne ya basu umurni kafin su sanar da al’ummar Najeriya zabin nasu.
Kuma yace aun zabi La Long ne domin sunada yakinin cewa shine kadai zai taimakawa Tinubu da Shettima su lashe zaben shekarar 2023.
Inda kuma yace aun zabi Fetus Keyamo a matsayin mai magana da yawun Tinubu na kungiyar kamfe, sai Hannatu Musa mataimakiyarsa.