Jam’iyyar APC Ta Dage Ranar Gudanar Da Zaɓukan Fidda Gwani Na ‘Yan Takarar Kujeru Daban-daban
Daga Sani Twoeffect Yawuri
Jam’iyyar ta APC ta fitar da sanarwar canza lokutan ne a jiya Laraba.
Kamar dai yadda jadawalin ya nuna, an dage fara zaben daga ranar Juma’a 20/5/2022 zuwa ranar 26/5/2022.
Za avgudanar da zaɓukan ne kamar haka a bisa sabon jadawalin:
1. Ranar Alhamis 26/5/2022: Zaben fidda gwanin Gwamnonin Jihohi da Ƴan Majalisun tarayya wato House of Representatives
2. Ranar Juma’a 27/5/2022: zaben fidda gwani na Sanatoci da ƴan majalisun Jihohi wato Senate da State House of Assembly
3. Ranar Lahadi da Litinin 29/5/2022 da 30/5/2022: Babban taro na musamman domin zaɓen fidda gwani na shugaban ƙasa