Jam’iyyar APC reshen jihar Ekiti ta dakatar da gwamnan jihar bisa zargin yiwa jam’iyyar zagon kasa.
Hakan ya fito ne daga sanarwar da jam’iyyar ta fitar da safiyar yau, Juma’a. Sanarwar wadda ta samu saka hannun daya daga cikin shuwagabannin jam’iyyar, Tony Adeniyi ta zargi Gwamna Fayemi da yiwa APC zagon kasa musamman a zaben jihar Edo da aka kammala kwanannan.
APC tace kwanaki kadan kamin zaben Ekiti, gwamna Fayemi yayi zama da wasu shuwagabannin PDP inda aka shiryawa APC zagon kasa a zabsn Edo.
Sannan kuma jam’iyyar ta zargi gwamnan da goyon bayan gwamnan jihar Oyo duk da cewa dan PDP ne.