Kimanin mambobin jam’iyyar APC mai mulki a kasa 5,000 ne suka sauya sheka zuwa jam’iyyar PDP a kananan hukumomin Matazu da Musawa na jihar Katsina.
Rahotanni sun ce mutanen sun bi shugaban nasu Hon. Ali Maikano, ya koma babbar jam’iyyar adawa saboda musgunawa da shugabannin jam’iyyar APC suka yi musu a lokacin zaben fidda gwanin da ta gudanar a yankin.
An tattaro cewa Ali Maikano ya tsaya takarar dan majalisar tarayya mai wakiltar mazabar Matazu/Musawa a karkashin jam’iyyar APC amma bai samu nasara ba, don haka ya bayyana ficewarsa daga jam’iyyar saboda abin da ya bayyana a matsayin bijerewa tsarin dimokradiyya wanda ya hana shi samun tikitin tsayawa takara.
Da yake karbar wadanda suka sauya sheka a garin Matazu, shugaban jam’iyyar PDP na jihar, Hon. Salisu Yusuf Majigiri, ya ba su tabbacin yin adalci da daidaito a sabuwar jam’iyyarsu, ya kuma kara da cewa PDP ta kasance jam’iyyar da ba za a iya rabuwa da ita ba kuma yayan jam’iyyar suna da hadin kai a jihar.