Jam’iyyun siyasa hudu a jihar Yobe sun nuna adawa kan cewa ba za su shiga zabukan kananan hukumomin da aka shirya gudanarwa ba a jihar a watan Fabrairun shekarar 2021.
Sakatare na Inter Advisory Council (IPAC) reshen jihar Yobe, Adamu Muhammad Babangida shine ya furta hakan a wata hira da yayi da manema labarai a Damaturu dake babban birnin jihar.
Babangida ya yi zargin cewa tsarin zaben da aka shirya babu adalci.
A cewarsa jam’iyyu huda dake jihar sun yanke shawarar ficewa daga zabukan domin baza ai musu adalci ba.
To dama ai abun haka yake ai bamu ba wata jam,iyya a yobe sai Apc ai gwandama ku ki Fitowar domun baku da magoya ba masha Allah