fbpx
Monday, June 27
Shadow

Janar Buratai ya bayar da shawarar yanda za’a magance matsalar tsaro

Tsohon shugaban sojojin Najeriya, Janar Tukur Yusuf Buratai ya bayar da shawarar cewa, a yi amfani da hanyoyin sulhu wajan magance matsalar tsaron dake damun Najeriya.

 

Ya kuma bayyana cewa, amfani da makaman da aka kera a Najeriya zai taimaka matuka wajan magance matsalar.

Buratai ya bayyana hakane a wajan wani taron da aka yi a Arewa House inda yace ya kamata a saka Shuwagabannin Al’umma da suka hada da sarakunan gargajiya da kuma malamai wajan magance matsalar.

 

Yace suma mutanen gari na da rawar da zasu taka wajan ganin an magance matsalar tsaron da ake fama da ita.

Leave a Reply

Your email address will not be published.