fbpx
Thursday, May 26
Shadow

Jerin ministocin da wannan umarni zai iya shafa

Shugaba Muhammadu Buhari na Najeriya ya umarci ministocinsa masu son takara su yi murabus daga nan zuwa 16 ga watan Mayu.

Ministan yaɗa labarai na ƙasar Lai Mohammed ne ya sanar wa da manema labarai hakan bayan kammala taron majalisar zartarwa na mako-mako a ranar Laraba da aka yi a fadar shugaban ƙasa da ke Abuja.

Tun da fari a ranar 25 ga watan Fabrairun 2022 Shugaba Buhari ya bukaci ‘yan majalisa tarayyar ƙasar da su hanzarta yin gyara ga sashe na 84 na dokar wanda ya tanadi haramta wa masu rike da mukaman gwamnati jefa kuri’a a zaben shugabannin jam’iyya ko kuma na ‘yan takara.

Shugaban ya nemi hakan ne a lokacin da ya sanya hannu kan sabuwar dokar zabe ta kasar wadda aka dauki tsawon lokaci ana ka-ce-na-ce a kanta.

Chibuike Rotimi Amaechi – Ministan sufuri

Godswill Akpabio – Ministan harkokin Neja Delta

Ogbonnaya Onu – Ministan kimiyya da fasaha

Chris Ngige – Ministan ƙwadago

Emeka Nwajiuba – Ƙaramin ministan ilimi

Timipre Sylva – Ƙaramin ministan albarkatun man fetur

Abubakar Malami – Ministan Shari’a

Paulline Tallen – Ministar harkokin mata

Akwai yiwuwar wannan umarnin zai yi tasiri ga yanayin gudanar da gwamnati sakamakon adadi mai yawa da wannan umarnin na Shugaba Buhari zai iya shafa.

Sai dai mai magana da yawun shugaban ya ce wannan lamarin ba zai shafi harkokin gudanar da gwamnati ba.

Ana sa ran duka jam’iyyu za su gudanar da zaɓen fitar da gwanin su nan gaba a wannan watan.

Dan sauke manhajar hutudole a wayoyin ku. Sai a bi wannan link din na kasa:

Leave a Reply

Your email address will not be published.