A lokacin da shugaban kasa, Muhammadu Buhari ya karbi mulki a shekarar 2015, ‘yan Najeriya da yawa sun cika da murna musamman saboda alkawarin da yayi na cewa zai yi yaki da rashawa da cin hanci.
A wata hira da CNN ta yi dashi, shugaban a wancan lokacin ya bayar da tabbacin cewa, lallai duk wanda aka kama yaci kudin gwamnati sai yayi amansu ko da kuwa a jam’iyya me mulki yake.
Saidai ba haka zancen yake ba, a takaice dai wanda a lokacin PDO ma ake zargin sun saci dukiyar kasa, sai gashi a mulkin shugaban kasa, Muhammadu Buhari ana ta musu afuwa, musamman wadanda suka koma jam’iyyar APC.
Adama dai tsohon shugaban jam’iyyar na APC, Adams Oshiomhole yayi subul da baka inda yace komai laifinka idan ka shiga jam’iyyar APC an yafe.
Misalin mutanen da ake zargi da cin kudin talakawa amma a mulkin shugaba Buhari aka yafe musu ko kuma aka wofintar da maganar sune:
Sanata Danjuma Goje, an zargi Sanata Goje da cin Naira Biliyan 5. Saidai babban lauyan gwamnati kuma ministan shari’a, Abubakar Malami ya dakatar da shari’ar da akewa Goje bayan da Gojen ya amince ya janyewa Ahmad Lawal neman takarar kakakin majalisar dattijai.
Kwanaki 29 bayan da Goje ya gana da shugaba Buhari akan maganar, aka dakatar da shari’ar da ake masa ta cin Biliyan 5.
Karin wani misali shine na tsohuwar ministar harkokin sufurin jiragen sama, Stella Oduah wadda ita kuma ake zarginta da cin Biliyan 7.9.
Saidai itama ana tsammanin ministan shari’a, Abubakar Malami ya dakatar da shari’ar da ake mata inda daga baya ta koma jam’iyyar APC.
Hakanan akwai kuma shugaban APC na yanzu, sanata Abdullahi Adamu wanda tsohon gwamnan jihar Nasarawa ne wanda shima ana zarginsa da cin Naira Biliyan 15, har ma an kaishi kotu da zarge-zarge 149.
Hakanan akwai dansa Nuraini wanda shi kuma ake zarginsa da cin Miyan 92, amma bayan da ya koma APC, shima maganar ta bace.
Hakanan shima sakataren jam’iyyar APC wanda tsohon Mataimakin gwamnan jihar Osun ne kuma tsohon sanata, Senator Iyiola Omisore an zargeshi da cin Biliyan 1.3, amma yana komawa APC shima maganar ta bace.
Hakanan akwai tsohon gwamnan jihar Abia, Uzor Kalu wanda ake zarginsa da cin Biliyan 7.1, shi har ma an daureshi amma bai jima ba ya fito daga gidan yarin ya kuma koma jam’iyyar APC, daga nan maganar ta bace.
Na baya bayannan sune tsohon gwamnan jihar Taraba, Jolly Nyame da tsohon gwamnan jihar Filato, Joshua Dariye.
‘Yan Najeriya da yawa na mamakin wannan abu dan kuwa ya sabawa alkawarin yaki da cin hanci da gwamnatin shugaban kasa, Muhammadu Buhari ta yi.