fbpx
Saturday, August 8
Shadow

Ji abinda Messi yace da aka tambayeshi zai ba Cristiano Ronaldo kwallo idan suka buga wasa tare?

Kaftin din Barcelona Lionel Messi ya kasance abokin hamayyar tauraron Juventus Cristiano Ronaldo fiye da shekaru goma da suka gabata.

 

Manema labarai Mundo Deportivo sun tambaya Messi cewa shin idan suka yi wasa tare da Ronaldo a kungiya daya zai bashi kwallo?, sai Messi yace yana tunanin hakan, daga baya kuma sai yace eh zai bashi.

Ronaldo ya cika shekara ta 35 a watan fabrairu kuma yana kokari sosai a wannan kakar wasan yayin da yayi nasarar jefa keallaye 25 a wasanni guda 32 daya buga. Kuma tsohon tauraton Madrid din yayi nasarar cin kwallo a wasanni har guda 11 a jere a wannan kakar wasan.

 

Shi kuma Messi yayi nasarar cin kwallaye guda 24 kuma ya taimaka wurin cin kwallye guda 16 a wasanni guda 31 daya buga.

 

 

Messi ya yaba Cristiano Ronaldo yayin yake cewa a shi kwararren dan wasa ne kuma yana in har ya buga wasa yana cin kwallo.

Dan sauke manhajar hutudole a wayoyin ku. Sai a bi wannan link din na kasa:

https://play.google.com/store/apps/details?id=hdlabarai.aplibwxLeave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *