fbpx
Thursday, May 26
Shadow

Ji abinda Nnamdi Kanu ya fadawa gwamna Soludo akan ‘yan kungiyar IPOB

Gwamnan jihar Anambra, Soludo ya ziyarci shugaban ‘yan kungiyar Biafra ta IPOB wanda ke tsare a hannun ‘yan sandan DSS, watau Mazi Nnamdi Kanu.

Inda yace ya ziyarce shine domin a shawo kan matsalar tsaron da kudu masu gabashin kasar nan ke fama da shi.

Yace Kanu yayi Allah wadai da wa’yanda ke kashe mutane babu dalili kuma suna fakewa da sunan kungiyar IPOB.

Kuma a karshe Kanu yace idan har ya samu dama to zai wayar da kan mabiyanshi su daina tayar da hankulan al’umma.

Leave a Reply

Your email address will not be published.