A jiya, Talata dai an samu hukunce-hukuncen kotu biyu masu karo da juna wanda daya na babbar kotun tarayya ce dake Kano data ce a sauke Sarki Muhammad Sanusi II saga sarautar Kano.
Mai shari’a, S. Amobeda ne ya bayyana hakan a hukuncin daya fitar inda yace a mayar da Aminu Ado Bayero a matsayin sarkin Kano.
Saidai itama babbar kotun Kano karkashin mai shari’, Amina Aliyu tace Sarki Muhammad Sanusi II ne sarkin Kano inda kuma tace Sarki Aminu Ado Bayero ya daina bayyana kansa a matsayin sarkin Kano.
Saidai duk da wannan hukunci, Sarki Aminu ya ci gaba da zama a karamar fadar dake Nasarawa inda yace ci gaba da ayyana kansa a matsayin sarkin Kano.
Rahotanni sunce har yanzu akwai jami’an tsaro da aka girke a gidan Nasarawa wanda kuma suna hana ma mutane bin hanyar sai wanda ya zamarwa dole.