fbpx
Sunday, June 26
Shadow

Ji abinda Sheik Ibrahim na Kaduna yace zasu yi idan Tinubu ya zabi kirista a matsayin abokin takararsa

Sheik Ibrahim Aliyu na jihar Kaduna ya gargadi APC da dan takararta na shugaban kasa, Bola Tinubu akan zabar Kirista a matsayin abokin takararsa na zaben 2023.

Yayin da yanzu awanni 48 ne suka ragewa ‘yan takarar dasu bayyana abokan takararsu kamar yadda hukumar zabe ta INEC ta bukata.

Inda malamin yace idan har Bola Ahmad Tinubu ya zabi Kirista a matsayin aboki takararsa tofa APC ta kamo hanyar da bata bullewa kuma baza tayi nasara ba.

Sannan malamin yayi barazanr hana Musulmi zabar jam’iyyar ta APC inda kuma ya caccaki gwamonin Arewacin Najeriya Musulmai.

Leave a Reply

Your email address will not be published.