Dan takarar shugaban kasa na jam’iyyar APC, Asiwaju Bola Ahmad Tinubu ya zabi dan arewa Musulmi a matsayin abokin takararsa, Kashim Shettima.
Amma sai dai wasu ‘yan Najeriya basu goyi bayan hakan ba inda suka ce kamata yayi ya zabi kirista daga arewacin kasar.
A yau ranar lahadi ne ya bayyana sanatan jihar Bornon a matsayin abokin takararsa na zaben shekarar 2023 a Daura bayan ya kaiwa shugaba Buhari ziyara.
Kuma hatta wasu daga cikin hannu da tsaki a jam’iyyar sun fifita zabar Kirista akan Kusulmi.