fbpx
Monday, August 15
Shadow

Ji bayani dalla-dalla yanda ‘yan Bindiga suka kaiwa tawagar motocin shugaba Buhari hari

Gwamnatin Najeriya ta bayyana damuwarta da bacin ranta kan wani hari da aka kai wa ayarin motocin Shugaba Muhammadu Buhari a kusa da garin Dutsinma na Jihar Katsina.

Wata sanarwa da Mallam Garba Shehu, mai magana da yawun shugaban kasar ya fitar ta ce an kai harin ne kan ayarin motoci dauke da jami’an da ke wa shugaban hidima yayin da suke kan hanyarsu ta zuwa Daura gabanin bikin Babbar Sallah.

Sanarwar ta kuma ce shugaban na Najeriya ba ya cikin ayarin motocin.

Garba Shehu ya kara da cewa wasu mahara da ba a tantance ko su wane ne ba sun yi wa ayarin wuta kwanton-bauna, kuma sun bude wa jami’an wuta.

Cikin jami’an tsaron akwai ‘yan sanda da sojoji da kuma na DSS.

Cikin jami’an akwai wadanda za su tarbi shugaban na Najeriya idan ya isa garin Daura, da masu ba shi tsaro da masu masa hidima, da kuma ‘yan jarida.

A karshe sanarwar ta ce ana ba wasu mutum biyu cikin jami’an da ke cikin ayarin motocin kulawa a asibiti, kuma sauran jami’an sun isa garin Daura.

Dan sauke manhajar hutudole a wayoyin ku. Sai a bi wannan link din na kasa:

Leave a Reply

Your email address will not be published.