fbpx
Thursday, July 7
Shadow

Ji bayanin yanda ake dannewa kananan sojojin Najeriya hakkokinsu

Yayin da hukumomin sojin Najeriya suke watsi da wani zargi da kananan sojoji ke yi wa manyansu na tauye musu hakkoki, wadansu bayanai da BBC ta samu na cewa akwai lokutan da ake samun jinkirin biyan kudaden alawus, kuma idan ba a yi sa’a ba sun makale ke nan.

Masana sha’anin tsaro dai na cewa rashin biyan hakkokin jami’an tsaron, na iya sanyaya gwiwar sojojin da ke fagen fama.

Wadansu kananan sojoji ne suka rubuta budaddiyar wasika ga shugaba Buhari suna zargin cewa ana cinye musu kudadensu na alawus.

A martanin da ta mayar dangane da zargin danne hakkin kananan sojojin, rundunar sojin kasa ta Najeriya ta ce ana biyan jami’an ne ta wani tsari na asusun bai-daya.

Ta ce a bisa wannan tsari ba ta yadda za a ware wani soja a yi masa kwange a kudinsa na alawus.

To amma a binciken da BBC ta yi ta gano cewa kananan sojojin suna korafi ne kan kudaden alawus da ake ware musu na kwanan daji, a lokacin da suke bakin-daga, idan an tura su aiki.

Wani soja da BBC ta tattauna da shi, ta sirri ya ce, ana biyansu naira dubu 45 ne a duk wata, idan suna bakin-daga.

Sai dai ya ce inda Gizo ke sakar shi ne, wajen biyan musamman ma idan kana sabon zuwa kamar yadda ya ce: ”To amma a dubu 45 din sai ka ga ka zo sabo-sabo nan ne aka fi samun matsalar.”

Sai ka ga ka yi wata biyu, uku wani ma ya kai biyar ba ya samunsu.” In ji shi.

Ya ce a irin haka ana tara sunayen sai kwamandan ya ce ku tattara sunayen wanda ya san yana da matsalar biya.

”Ni nawa an rike min wajen wata hudu haka amma sauran duka sun biya ni da suka bude.

“Sai da na yi wajen wata biyar to a wata na biyar din sai suka fara biya na to wancan wata hudu da suka wuce duka ba su ba ni ba.” In ji sojan.

Dangane da kayan sarki kuwa, sojan ya ce a yanzu ba a ba su sai dai su saya, amma a da ana raba musu ne.

Sai dai kuma jami’in ya ce galibi kyautata wa ko akasin haka, abin ya dogara ne ga kwamandanku, kasancewar wasu masu kirki ne wasu kuma marassa kirki ne.

To amma kuma ya ce a yanzu rayuwar sojojin ta fara inganta tun bayan da aka nada sabon hafsan sojin kasa na yanzu.

Ra’ayin masu sharhi

Masu sharhi kan harkokin tsaro irin su Manjo Muhammad Bashir Galma (mai ritaya) na ganin dole ne a rika samun irin wadannan korafe-korafe na sojojin idan dai akwai kudi.

Saboda ba a taru an zama daya ba a shugabannin, wasu suna da kiriki wasu kuwa bata-gari ne.

Ya ce dole ne a bincika aga inda lamarin yake faruwa domin a yi gyara, kasancewar rashin yin gyaran na iya raunana kwarin guiwar sojojin, tun da suna da iyalai da kuma bukatunsu.

Game da barazanar da wasu sojojin ke yi ta yin yajin aiki, masanin tsaron ya ce ai yajin aiki ko bore babban laifi a aikin soja ko dan-sanda, wanda ake hukuntawa da dauri mai yawa ko ma harbewa.

Ya ce a aikin soja ko dan-sanda tun kafin ma ka shiga za a gaya maka ba zanga-zanga, domin babban laifi ne.

Dan sauke manhajar hutudole a wayoyin ku. Sai a bi wannan link din na kasa:

Leave a Reply

Your email address will not be published.