Dan takarar shugaban kasa na jam’iyyar PDP, Alhaji Atiku Abubakar ya soki babban abokin adasarsa na zabe mai zuwa wato dan takarar APC, Asiwaju Bola Ahmad Tinubu.
Atiku Abubakar ya bayyana hakan ne a Arise TV, i da yace babban abinda ya fara hada shi fada da Tinubu shine, tsohon gwamnan jihar Legas din na son tsayar da Musulmi da Musulmi a takarar shugaban kasa.
Wanda shi kuma yake ganin hakan ba daidai bane, Atiku yace sun fara samun sabani ne a shekarar 2007 lokacin daya bayyana Ben Obi a matsayin abokin takararsa na zaben shugaban kasa a jam’iyyar Action Congress.
Inda yace Tinubu ya nemi ya zabe shine kawai su tsaya takarar tare amma sai yaki amincewa, kuma ya bar jam’iyyar ne a shekarar 2011 bayan sun sake samun sabani ya koma PDP.