fbpx
Friday, May 27
Shadow

Ji labarin garin da ake aurar da ‘yan mata suna da shekaru 12 a Arewacin Najeriya

A Garin Agyema na jihar Nasarawa ana aurar da ‘yan mata tun suna da shekaru 12 da haihuwa.

 

Wasu kuma 13, a yayin da suka shekara 16 wasu na da ‘ya’ya 2 wasu ma 3.

 

Mata suna rigan maza kaiwa da balaga, sukan balaga a tsakanin shekaru 10 zuwa 14 da haihuwa, wasu ma kan balaga suna da shekaru 8 da haihuwa.

 

Mafi bayyanar alamun balaga ga diya mace shine aga nonuwa a kirjinta. Sai kuma sauran sassan jikinta suma zasu fara habaka, kamin daga baya ta fara jinin al’ada.

 

Shugaban kauyen Agyema, Chief Godiya Aitonu, ya bayyana cewa, talauci na daya daga cikin dalilan da suke sanya ana aurar da mata da wuri a garin.

 

Yace kuma gashi basu da ci gaban azo a gani.

 

Karanta wannan  Delegates 2 ne suka zabeni ba tare dana basu ko sisi ba amma guda 300 sun kirani kowanne na cewa shine ya zabeni>>Sanata Shehu Sani

Yace yawanci sana’arsu itace noma amma idan suka noma abin, bama su iya kaishi kasuwa saboda rashin kyawun hanya, hakan yasa saidai abincin ya lalace, wanda hakan kuma ya sanya mutane da yawa basa son yin noman.

 

Wani malamin addinin musulunci a Lafiya, Imam Yusuf Saidu ya bayyana cewa, addinin islama ya amince da aurar da mace kamin ta kai shekaru 18.

 

Yace amma maganar kwanciyar aure, sai mijin ya lura matar tasa ta kai shekarun balaga kamin ya kusanceta.

 

Yace kuma dole wanda za’a baiwa irin wannan matar sai ya kasance Musulmi, wanda kuma zai iya kulawa da tarbiyya da ilimin matar tasa.

Dan sauke manhajar hutudole a wayoyin ku. Sai a bi wannan link din na kasa:

Leave a Reply

Your email address will not be published.