Rahotanni sun bayyana cewa, Tsohon Mataimakin shugaban kasa, Alhaji Atiku Abubakar na son daukar Emeka Ihedioha a matsayin mataimakinsa.
Saidai jaridar Vanguard tace ba shi kadai bane sunansa ke gaban Atiku yana son tantancewa dan dauka.
Saidai shine ake kyautata zaton yafi sauran wanda Atikun ke tantancewa alamun samun wannan mukami.
An bayyana cewa, Ihedioha na da alaka me kyau sosai da tsohon mataimakin shugaban kasar.