Rahotanni sun nuna cewa, Gwamnan jihar Rivers, Nyesome Wike da tsohon gwamnan jihar Ekiti, Ayodele Fayose suna shirin cin amanar Atiku suna goyon bayan dan takarar shugaban kasa na APC, watau Bola Ahmad Tinubu.
Hakan zai tabbata ne idan Tinubu ya samu tikitin takarar shugaban kasa na jam’iyyar APC.
Saidai shi kanshi Tinubun da alama ba lallai ya kai labari ba dan tun yanzu ya fara maganganun dake nuna alamar karaya da lamarin inda yake nuna cewa, shugaba Buhari ya ci amanarsa.
Saidai rahoton Vanguard ya nuna cewa, ba Shugaba Buhari bane be son Tinubu, na kusa da shugaban kasar ne basa sonsa.