fbpx
Wednesday, August 10
Shadow

Ji yadda aka gudanar da shari’ar wani dan jihar Zamfara daya auri jikarsa har suka hayayyafa da ita

Kotun Shari’a dake karamar hukumar Tsafe a jihar Zamfara ta dage karan Musa dan shekara 57 zuwa ranar 25 ga watan Yuli, wanda aka maka a kotu kan auren jikarsa daya yi.

Musa yaki amincewa ya saki jikar tasa Wasila ‘yar shekara 37 wadda ya aura shekaru 23 da suka gabata kuma sunada yara guda takwas.

Hukumar Hisbah ce ta shigar da wannan karan kotun ta hannun lauyanta Sani Muhammad inda shima mutumin da jikar tasa lauyansu Ayuba Abdullahi ya wakilce su.

Karanta wannan  Najeriya ta zamo kasa ta hudu a cikin jerin kasashen da suka fi karbar bashi a bankin duniya na shekarar 2022

Shari’ar tayi zafi sosai har ta kaiga luyan masu shigar da kara ya karanto Aya a cikin Alkur’ani data haramta hakan, kuma alkali Mahe ya dage wannan karan izuwa 25 ga watan Yuli.

Dan sauke manhajar hutudole a wayoyin ku. Sai a bi wannan link din na kasa:

Leave a Reply

Your email address will not be published.