fbpx
Monday, August 15
Shadow

Ji yadda malamin Poly ya koma kwandasta saboda makarantar ta hana shi albashi na tsawon watanni

Wani malamin makarantar Polytechnic ta Rumuola dake jihar Patakwal, Zoe Toumunotonye ya bayyana yadda makaranyar taci zarafinsa kuma taki biyanshi albashi na tsawo watanni shida.

Inda yace makarantar ta zarge shi da laufin aikata lalata da wata daliba wanda hakan yasa ta dakatar dashi na tsawon watanni uku domin tayi bincike.

Kuma bayan ta kammala binciken bata ce masa komai ba, wanda hakan yasa ya koma aiki har na tsawon watanni shida amma bata biyan shi albashi, kuma shi ke daukar nauyin ityalansa da ‘yan uwansa bakidaya.

Karanta wannan  Sau shida kungiyar malamai ta ASUU tayi yajin aiki a lokacin da Atiku ke mataimakin shugaban kasa

Saboda haka ya nemi aiki sama da kasa bai samu ba wanda hakan yasa ya zama kwandasta kuma shima da kyar ya samu don yawancin direbobin sunki daukarsa.

Dan sauke manhajar hutudole a wayoyin ku. Sai a bi wannan link din na kasa:

Leave a Reply

Your email address will not be published.