fbpx
Friday, August 12
Shadow

Ji yadda mata mai ihun karnuka da aka yiwa asiri ta mutu a jihar Ogun

Hukumar ‘yan sanda sun tabbatar da labarin wata mahaukaciya data ke ihun karnuka kuma ta kashe kanta a jihar Ogun.

Mai magana da yawun hukumar Oyeyemi Abinbola ne ya bayyana hakan ranar juma’a inda yace ana zargin ‘yan damfarar ‘Yahoo boys ne sukayi asirin kudi da matar kuma an kamasu.

Labarin ya kaiwa hukumar ‘yan sanda kuma sun kai matar asibiti da kyar tsirara inda suka kira mahaifanta.

Hukumar ta bayyana cewa bata ji dadin yadda bideyon matar ke yawo a kafafen sada zumunta ba kaya ba yayin da suke kokarin kamata, kuma sunce zasu kama wanda ya dauki bideyon suka wallafa a kafafen sada zumunta.

Leave a Reply

Your email address will not be published.