Hukumar ‘yan sandan jihar Adamawa ta bayyana cewa ta kama wata mata Caroline Barka ‘yar shekara 20 bayan ta kashe mijinta Dauda Barka da wuka.
Wannan lamarin ya faru ne a ranar juma’a a anguwar Tsamiya dake karamar hukumar Madagali, cewar ‘yan sanda.
Kuma Barka ta kashe mijin nata dan shekara 38 ne bayan ta aka masa wuka yayin da suke fada saboda yana kaiwa dare a waje kuma yana yin shaye shaye.