Hukumar Hizba a jihar Kano da ke arewacin Najeriya, ta kama wasu matasa takwas da ake zargi da kwacen waya a masalallacin al-Fur’an da ke karamar hukumar Nasarawa da ke jihar.
Kwamandan Hizba Sheikh Harun Ibn Sina, ya tabbatar da hakan ga manema labarai a ranar Talata.
Ya ce an kama wadanda ake zargin da ranar Allah suna shan muggan kwayoyi da sauran ababen maye a kusa da masallacin.
Ibn Sina ya bayyana dabi’ar matasan da haramtacciya da ba ta dace ba a wannan wata mai alfarma na Azumin Ramadan.
Ya yi kira ga jama’a su kara sanya ido da kai rahoton duk wani abu da suka ga ya na faruwa da bai gamsar da su ba, ko wani mutum, su kuma hukumarsu ba za ta yi kasa a gwiwa ba wajen daukar mataki da hukunta wanda aka samu da laifi.