fbpx
Friday, August 12
Shadow

Ji yanda jami’an tsaron gidan yari ke sakin masu laifi a samo matasa su yiwa masu laifin zaman gidan yari

Babban lauya kuma dan rajin kare hakkin bil’adama, Femi Falana ya bayyana cewa, matsalar tsaron Najeriya ba wai dauko sojojin haya bane zai magance ta.

 

Falana ya bayyana hakane a wajan ganawa da manema labarai ranar Alhamis.

 

Yace ana kwamacala sosai a gidan yarin Najeriya.

 

Yace me laifi zai aikata laifi a kaishi gidan yari, amma saboda wasu bata garin ma’aikatan gidan yarin sai a hada baki dasu a sakeshiba samo matasa a biyasu su mai zaman gidan yarin.

 

Yace wasu masu laifin kuma bama su zuwa gidan yarin, ana hada baki dasune da ma’aikatan kotu ne daga kotun kawai su tafi gida.

 

Yace a Legas kawai, an samu rahoto a shekarar 2005/2006 cewa muyane 199 da aka yankewa hukunci kan safarar miyagun kwayoyi basu yi zaman gidan yarinba.

Karanta wannan  Dalilin dayasa naki umurtar rundunar soji ta ceto fasinjonin jirgin kasa na jihar Kaduna, shugaba Buhari

 

Falana ya kara da cewa, shugaban kasa, Muhammadu Buhari ya sabawa doka sashe 305 na kundin tsarin mulki da ya ce duk jihar dake fama da matsalar tsaro a saka dokar ta baci a cikinta.

 

Yace kuma ya sabawa doka kan kin daukar matakin da ya dace wajan magance matsalar tsaron kasar.

 

Yace idan ana maganar matsalar tsaro, Najeriya a yanzu tana fuskantar yaki ne amma kuma Shuwagabannin sun kasa gane hakan.

 

Fala ya kara da cewa, bin yafi gaban dauki sojojin haya daga wata kasa.

Dan sauke manhajar hutudole a wayoyin ku. Sai a bi wannan link din na kasa:

Leave a Reply

Your email address will not be published.