Al’ummar garin Goya da ke karamar hukumar Funtua a jihar Katsina ta arewacin Najeriya sun tsinci kansu cikin wani yanayi na fargaba sanadin artabun da suka yi da jami’an tsaro a makon da muke ciki.
Bayanai sun ce al’amarin ya faru ne bayan samamen da ‘yan sanda suka kai musu tare da yin harbe-harben kan mai-uwa-da-wabi.
Yayin samamen, mutanen garin sun zargi ‘yan sanda da yin harbin da ya yi sanadin kashe mutum ɗaya da raunata wasu tare da farfasa ababen hawa.
Sai dai ‘yan sanda sun ce mutanen garin ne suka fara auka musu da sara da jifa al’amari da ya janyo mutuwar jami’insu.
Bayanai sun ce an samu hantsaniya tsakanin ‘yan sanda da mutanen garin tun ranar 23 ga wannan watan, bayan da ‘yan sanda suka je wurin neman wani mutum.
Mazauna garin sun ce sun ga wasu mutane da daddare a cikin wata mota wadanda ba su yi kama da jami’an tsaro ba.
Wani mutum ya ce dama suna cikin fargaba saboda ‘yan bindiga sun ce za su kai musu hari.
“Sun je gidan wani ne da suke zargi infoma ne watau mai tseguntawa ‘yan bindiga bayanai, ana cikin tsoro dama, mutane suka zo suka ce mene ne bahasi, kawai sai suka kama harbi” in ji shi.
A cewarsa harbin da suka yi shi ne ya tabbatarwa mazauna garin da cewa lalle wadannan mutane ɓarayi ne. Ya kuma ce mazauna garin sun lura cewa babu wata shaida da ta nuna cewa su jami’an tsaro ne kuma motar da suka zo da ita ba ta da lamba.
Sai bayan da aka kai rahoto Funtua sannan aka gano cewa ashe jami’an tsaro ne kamar yadda mazaunin garin ya bayana:
“An kira area commander ya ce bai san da zuwansu ba, an kira duk wadanda suka kamata sun ce ba su san da zuwansu ba,” in ji shi.
Wani mazaunin garin na Goya ya kuma shaida wa BBC cewa hatsaniyar ta shafi wasu ‘yan uwansa biyu wadanda ya ce suna tsare a hannun jami’an tsaro
“Mun yi rubutu mun yi statement sun ba mu mun sa hannu cewa dukannin mutanen da suka yi wannan abu za a yi kokari a kawo su. Daga baya suka shigo gari babu zato babu tsammani kuma lokacin da suka motar dan uwana sun bi sun farfasa gilasanta, kakarmu sun shiga har dakinta sun jefa mata hayaki mai a hawaye,” in ji shi.
‘Da gangan suka far wa ‘yan sanda’
Sai dai rundunar ‘yan sandan ta jihar Katsina ta ce da gangan mutanen garin suka hana jami’an tsaro gudanar da aikinsu.
Kakakin rundunar ‘yan sandan SP Gambo Isa ya ce sun rasa jami’in dan sanda daya sanadin harin da mazauna garin suka kai musu.
“Sun samu tirjiya inda mutane garin suka yi ca a kansu kuma shugaban ita wannan tawaga da ake kira Inspector Sada Abubakar ya yi kokarin yi musu bayani amma mutanen garin suka far masa, aka yi ta saransa da adda har suka hallaka shi,” in ji shi .
Ya kuma karyata ikikarin da mazauna garin suka yi a kan cewa jama’in tsaron ba ya sanye da inifom. Ya ce jam’in da aka kashe yana sanye da kayan-sarki.
Rundunar ‘yan sandan jihar Katsina ta ce mutum fiye da 30 ne aka kama amma an saki sama da 19 daga ciki, kuma ana tsare da tara daga cikinsu.
Ta kuma ce za a gurfanar da su gaban kotu bayan kammala bincike nan ba da jimawa ba.
BBChausa.