Wani likita daga kudancin Najeriya ya bayyana cewa ya je aiki Arewa inda ya shafe watanni 3 kamin ya tafi kasar Ingila.
Yace da gangan idan aka kawo mai marasa lafiya dai ya rika barinsu suna mutuwa.
Yace ya ji dadin hakan kuma yaso ace ya kashe fiye da wadanda ya kashe, likitan daga kudancin Najeriya me suna Christopher Uche-Ayodeji ya bayyana cewa yayi hakan ne saboda kisan wata abokiyar aikinsa da aka yi a dhekarar 2015 a jihar Bauchi.
A confessed Murderer;Security agencies should launch an urgent investigation and bring him to justice. pic.twitter.com/t1GK8NLexd
— Senator Shehu Sani (@ShehuSani) May 13, 2022
Yace mahaifiyarta ta yi kuka sosai amma ya mata alkawarin dai ya daukar mata fansa kuma yayi hakan.
A martaninsa, Sanata Shehu Sani yace ya kamata a kamo wanda yayi wancan abin tunda gashi ya fada da kansa a hukuntashi.