fbpx
Thursday, May 26
Shadow

Ji yanda wani mutum ya baiwa abokinsa dubu 20 dan yayi kashi kashi a masallaci a Kaduna

Kotun shari’ar musulunci a jihar Kaduna ta daure mutane 2 masu sunan Nura Usman da Adamu Dauda saboda yin kashi a masallaci.

 

An zargi mutanen da cewa, sun kawo tashin hankali rudani tsakanin mutane.

 

Mai shari’a, Rilwanu Kyaudai ya daga shari’ar zuwa ranar 28 ga watan Afrilu.

 

Dansanda me gabatar da kara ya bayyana cewa, Dauda ya ce zai baiwa Dubu 20 idan yayi kashi a masallaci inda shi kuma ya aikata hakan.

 

Saidai dukansu sun musanta wannan zargi kamar yanda kamfanin dillancin labaran Najeriya, NAN ya ruwaito.

Leave a Reply

Your email address will not be published.