Wata matar aure dake da saurayi a waje, ta rika cin amanar mijinta ta hanayar dafa abinci ta kaiwa saurayin nata ba da sanin mijinta ba.
Daga baya dai mijin ya gane kuma ya saketa.
Bayan ta gama idda sai ta auri wancan saurayin da ta ke kaiwa abinci lokacin tana gidan tsohon mijinta.
Aikuwa ashe bata san yana dukan mata ba, ya rika lakada mata dukan kawo wuka, dole ba azziki ya saketa.
Sai kuma gashi yanzu ta dawo tana neman tsohon mijinta ya mayar da ita.