‘Yan Bindiga sun kashe abokin tsohon ministan yada labarai, Labaran Maku, watau Zakari Umaru-Kigbu.
A hirar tsohon ministan da manema labarai na Punchng, ya bayyana musu cewa abokin nasa tun suna matasa suke tare.
Yace sun hadu ne a Legas daga nan kuma abotarsu ta yi karfi. Ya kara da cewa, ‘yan Bindiga sun je gidansa suna kokarin balle kofa dan shiga.
Sai ya kira sojoji da ‘yansanda, amma sai ‘yansandan suka aika da ‘yansanda 2, yace ko da suka je suka ga ‘yan Bindigar dauke da makaman da suka fi nasu sai suka tsere.
Yace kamin zuwan sojoji kuwa, tuni ‘yan Bindigar sun kasheshi sun kuma tafi da yaransa 2, yace yana fatan Allah ya ji kansa.