fbpx
Thursday, June 30
Shadow

Jiga-jigan APC sun ce gaba dayan ‘yan takarar jam’iyyar su hakura su goyawa Goodluck Jonathan baya

Jiga-Jigan Jam’iyyar APC sun nemi gaba dayan masu neman takarar shugabancin Najeriya su hakura su goyawa Goodluck Jonathan baya.

 

Masu wannan yunkuri wanda dan uwan Buhari, Mamman Daura ke jagoranta sun bukaci hakanne dan ganin Ganin Goodluck Jonathan ya sake zama shugaban Najeriya.

 

Kwanannan ne dai aka ga Mamman Daura ya je har gids ya gana da Goodluck Jonathan amma ganawar tasu ta sirri ce.

 

Majiyoyi da yawa sun bayyanawa Sahara Reports cewa, da wuya a yi zaben fidda gwani a APC, dan takarar bai daya kawai za’ayi.

Leave a Reply

Your email address will not be published.