Wani jigo a jam’iyyar APC wanda tsohon mataimakin shugaban jam’iyyar ne a yankin Arewa ta tsakiya, Ahmad Sulaiman Wambai ya bayyana cewa APC ta kashe makudan kudade wajan ganin ta lashe jihohi da dama.
A wata hira ds aka yi dashi a Sunnews, Wambai ya bayyana cewa a zabukan jihohin Imo Kwara, Zamfara da Benue da Gombe sai da tsohon shugaban jam’iyyar, Adams Oshiomhole ya baiwa kowane dan takarar gwamna Biliyan 1.
Sannan kowane dan takarar neman kujerar majalisar wakilai saida aka bashi Niliyan 20, su kuma ‘yan takarar majalisar Dattijai aka basu Miliyan 10 kowannensu.
Yace daga cikin Asusun jam’iyyar ne aka dauki wadannan kudade yace kuma jam’iyyar ta samu kudadenne daga sayar da fom din takarar da ta yi, yace ba’! Banza suka saka kudin sayen Fon din da tsada ba.
Ya kuma kara da cewa, Adams Oshiomhole ne shugaban jam’iyya da aka yi na farko a Najeriya da gwamnoni basu rika tara masa kudi ba. Yace dan takarar gwamnan Benue ne kawai aka baiwa Naira Miliyan 700.
Ya kuma kara da cewa dalilin da yasa vwamnonin suka jiyawa Oshiomhole baya saboda zaben shekarar 2023 na zuwa kuma shi yace babu wanda za’a maida dan lele su kuma gwamnonin suna son takarar shugaban kasa da ta mataimakin shugaban kasa.
Yace tunda Oshiomhole yake aikinsa shugaban kasa, Muhammadu Buhari bai taba masa katsalandan ba kuma da ace sauran wanda suke zagaye da shugaban kasar zasu yi koyi da halinsa da Najeriya ta ji dadi.