fbpx
Friday, May 27
Shadow

Jigon jam’iyyar APC na jihar Ribas ya tsallake rijiya da baya a wani yunkurin kashe shi da akayi

Wani jigon jam’iyyar APC kuma dan takarar gwamna a jihar Ribas, Prince Tonye Prince ya tsallake rijiya da baya a yunkurin kashe shi.

An tattaro cewa ana zargin ‘yan bindigar hayar su akayi ne domin sukai masa farmaki a gidansa da ke New GRA Fatakwal a safiyar Juma’a, 15 ga Afrilu.

Yarima mai jiran gado na Kalabari, wanda ke zama na hannun daman Ministan Sufuri, Rotimi Amaechi, ya tabbatar da faruwar lamarin a cikin wata sanarwa da ya fitar, inda ya ce ga dukkan alamu shi ne maharan ke nema ruwa a jallo.

Karanta wannan  Peter Obi ya fice daga jam'iyyar PDP

Ya ce bayan sun kutsa cikin gidansa ne maharan suka nufi dakinsa kai tsaye suka shiga inda suka tarar baya ciki.

Ya kara da cewa, ba su dauki wani abu mai kima a gidansa ba amma sun yi awon gaba da na’urar daukar hoton ta CCTV.

Dan sauke manhajar hutudole a wayoyin ku. Sai a bi wannan link din na kasa:

Leave a Reply

Your email address will not be published.