Tauraron dan wasan Manchester United, Cristiano Ronaldo ya taimakawa kungiyar tasa da kwallaye uku da doke Norwich daci 3-2 a gasar Firimiya.
Kwallayen da Cristiano Ronaldo yaci sun kasance na 21 daya ciwa United a wannan kakar, yayin da yanzu ya kasance yana cin kwallaye sama da 20 a kakanni 16 a jere.
Kuma hatrick din dayaci ta kasance ta 60 dayaci a harkarsa ta kwallon kafa, inda yaci 50 a kungiyoyi kuma yaci goma a kasarsa. Sannan kuma yaci kwallon free-kick ta 58 a harkarsa ta wasan tamola.