Hakan na kunshe ne a cikin wata sanarwa da Gwamnan yayi a daran litini bayan da majalisar dinkin duniya ta tabbatar da cewa cutar Coronavirus ta yi ajalin ma’aikacinta na lafiya guda a jihar ta Borno.
Dokar dai zata fara aiki daga karfe 10:30 na daran ranar laraba 22 ga watan da muke ciki.
Haka zalika gwamnatin jihar ta haramta duk wani taron jama’a har tsawan mako 2
Sai dai a cewar gwamnan dokar bata shafi masu kayan masarufi ba.