Rahotanni daga jihar Bayelsa na cewa jihar ta Bude guraren Ibada inda ta baiwa coci-coci masu manyan gine-gine su rika ibada da mutanen da basu wuce 200 ba.
Wannan na kunshene cikin sanarwar da shugaban kwamitin yaki da cutar Coronavirus/COVID-19 na jihar, Bangaren Coci, Fasto Samuel John Peters.
Sanarwar tace amm coci-coci ya zamana suna bin dokar nesa-nesa da juna da kuma samar da abin wanke hannu