Jihar Jigawa ta saka dokar kisa kan masu yiwa yara fyade.
Dokar ta tanadi cewa, duk wanda aka kama yawa yarinya da bata kai shekaru 10 fyade ba, za’a yanke masa hukuncin kisa ba tare da zabi ba.
Kwamishinan shari’a na jihar, Dr. Musa Adamu ne ya bayyana haka ga manema labarai.
Ya bayyana cewa a baya akwai dokar daurin rai da rai kan fyade amma a yanzu an kara data kisa kan duk wanda yawa yarinya fyade.