Gwamnatin jihar Jigawa tace ta rabawa mata masu ciki da kuma masu shayarwa har Naira Biliyan 192.96 a cikin watanni 7 da suka gabata.
Sakataren hukumar gyare-gyare na jihar, Ibrahim Rabakaya ne ya bayyana haka a wajan wani taro da aka yi a jihar Kano.
Raba kaya yace mata 5,740 ne suka amfana da tallafin inda yace sun aikawa kowace daga cikin matan Naira 32,000 da kuma 4,000 duk wata tsakanin watannin November na shekarar 2021 zuwa June na shekarar 2022.
Kamfanin dillancin labaran Najariya, NAN ya bayyana cewa, wadannan kudade an bayar dasu ne dan inganta rayuwar yaran da ake shayarwa da kuma ta iyayensu.