Friday, May 29
Shadow

Jihar Kaduna Ba Ta Shirya Bude Kasuwanninta Ba

Gwamnatin jihar Kaduna ta ce har yanzu ba ta sa ranar bude Kasuwannin jihar ba, saboda gudun yaduwar cutar coronavirus.

 

 

Shugaban hukumar kula da Kasuwannin jihar Kaduna, malam Hafiz Bayero ya ce da kyakykyawar manufa gwamnati ta rufa wadannan Kasuwanni.

 

Da yawan ‘yan kasuwan jihar Kaduna dai sun koka game da irin halin da su ka shiga biyo bayan kulle Kasuwannin jihar.

 

 

Ita dai gwamnatin jahar Kaduna ta ce don kare lafiya ta kulle wannan Kasuwanni, inji shugaban hukumar kula da Kasuwannin jihar Kaduna, malam Hafiz Bayero.

 

 

A jihar Kaduna dai, yanzu a makarantu ake cin kasuwa kuma a ranaku biyun da aka kebe don al’uma su fita kasuwa. Gwamnati kuma ta ce ta yi haka ne don tabbatar da hana cunkoson mutane a Kasuwanni.

Dan sauke manhajar hutudole a wayoyin ku. Sai a bi wannan link din na kasa:

https://play.google.com/store/apps/details?id=hdlabarai.aplibwxLeave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *