Gwamnatin jihar Kaduna ta bayar da umarnin yiwa Almajiran da aka mayar mata da su daga wasu jihohin Arewa dinkin Sallah.
Daya daga cikin Telolin da aka baiwa wannan aiki ne ya shaidawa shafin hutudole haka inda yace an basu unarnin yin dinkin akan lokaci dan Almajiran su samu yin kwaliyar Sallah da kayan.
Jihohin Arewa sun cimma matsayar mayar da Almajirai jihohinsu na Asali dan magance matsalar Almajirci inda suka sha alwashin saka Almajiran makarantun Boko.