fbpx
Wednesday, August 10
Shadow

Jihar Kaduna Ta Rufe Wasu Manyan Wuraren Kasuwanci Saboda taka Dokokin Coronavirus

Ma’aikatar Kasuwanci da kere-kere ta Jihar Kaduna ta rufe wasu manyan wuraren kasuwanci da ke aiki a jihar saboda kin bin ka’idojin coronavirus na jihar.

Kungiyar tilastawan ta ma’aikatan, wanda kwamishinan ma’aikatar, Idris Nyam ya jagoranta, yayin binciken a ranar Alhamis, ya sadu da mutane na cin abinci a gidajen abinci, wuraren burodi, wanda hakan ya sanya su keta ka’idojin cutar corona don sake buɗe guraren, kamar yadda yakamata ace suna kaiwa mutane gida ko kuma su siya,su tafi da shi tare da nisantar da jama’a da kuma shigar da garkuwa a tsakanin abokan ciniki da ma’aikata.
Guraren kasuwancin da aka rufe sun hada da shahararren gidan abincin Shagalinku, wanda ke Ali Akilu Road, Cake house, dake Sabon Tasha, Big Treat, Gidan abinci na 7 Stars, Gidan cin abinci na Baraka, da gidan abincin Naji Nice duka a kan titin Isa Kaita a cikin garin Kaduna.
Hakanan, otal din da aka kaima binciken, wadanda suka hada da Top Galaxy Hotels, (wurin yunkaya da mashaya), Sabon Tasha da Epitome Hotel (Bar / pool) a Barnawa, su ma ma’aikatar sun kulle su, don gudanar da budaddan mashaya, cin abinci a gurin da kuma watsi da nisantar juna.
Dangane da rahotannin Hukumar NCDC game da yaduwar cutar corona a Najeriya, jihar Kaduna ce a lamba ta takwas, tare da sama da 1289 mutanin da suka kamu.

Dan sauke manhajar hutudole a wayoyin ku. Sai a bi wannan link din na kasa:

Karanta wannan  Sanata Shehu Sani ya cewa gwamnonin da suka baiwa Buhari shawara ya sallami ma'aikatan da wuce shekara hamsi su fara kansu

Leave a Reply

Your email address will not be published.